Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa mutuwar da iyayen sa suka yi tun ya na kankane, da kuma haushin yadda ba su kai lokacin da za su ci moriyar sa a duniya ba, shi ne abin da ya fi bakanta masa rai a duniya.
Yace ganin irin yadda suka sha wahala da shi, ya so a ce Allah ya nuna musu lokacin da shi ma zai rika hidima da su.
Ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ake bikin cikar sa shekaru 81 a duniya a Cibiyar Tatro ta Marque Centre da ke cikin dakin karatun sa, a Ota, jihar Ogun.
Sai dai ya kara da cewa, kamar yadda wata karin maganar da Yarabawa ke yi, to ya san iyayen na san a can a cikin kabari su na murnar ganin yadda dan na su ya kai wata kololuwa nasara rayuwa.