Wasu mambobin Majalisar Tarayya biyu, Sanata Isa Misau da Kabiru Gaya, sun yi sa-in-sa jiya Laraba a Majalisar Tarayya sanadiyyar rikicin Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje da Sanata Rabi’u Kwankwaso.
Misau ya nemi majalisa da ta bayyana rashin jin dadin ta ga gangamin da Jam’iyyar APC ta yi a Kano inda aka tara dubun-dubatar ‘yan daba dauke da muggan makamai a wajen taron.
Ya bayyana cewa Kano na da matukar muhimmanci ga Arewa da kuma Najeriya baki daya. Kuma ya ce jihar ta hada iyaka da jihar sa, Bauchi.
Ya tunatar da cewa, “rikicin nan ya samo asali ne lokacin da Kwankwaso ya nemi ya gudanar da kai ziyarar sa a Kano, kuma ya rubuta wa Kwamishinan ‘Yan sandan Kano takardar sanarwa, amma aka shawarce shi da kada ya yi nasa taron.
“Ya Mai Girma Shugaban Majalisa, idan mu na zaune mu kallo a rika hana Sanata dan’uwan mu kai ziyara a jihar sa, kuma ba za mu yi magana ba, to fa ba mu kyauta wa junan mu ba.” Inji Misau.
“Zan son ka ga irin muggan makaman da aka rika walwali ana yawo da su a tsakiyar jami’an gwamnatin Kano. Tsoron da na ke kara ji, hanyar Kano ita ce kadai hanyar da mu ke bi idan za mu je ganin gida a Bauchi.
Sai dai kuma Sanata Kabiru Gaya da Sanata Barau JIbrin, duk ba su goyi bayan Misau ba. Jibrin ya zargi Misau da shiga shirgin da babu ruwan sa, da kuma hada baki da wani bangare domin ya haifar da rabuwar kawuna a Majalisar Dattawa.
Gaya ya ce matsalar Ganduje da Kwankwaso, matsala ce ta cikin gida, ba sai Misau ya shigo musu da ita a cikin majalisa ba.
Jibrin ya ce a baya masu rikicin biyu aminan juna ne. Kuma ana nan ana kokarin sasanta su a Kano.
Da shugaban majalisar Bukola Saraki ya nemi ya ji ta bakin sanata Kwankwaso a Majalisar, Kwankwaso ya fadi cewa ba shi da abin da zai ce game da abin da ya faru a Kano. Ganin haka sai shugaban majalisar ya dakatar da ci gaba da muhawara kan maganar a zauren majalisar.