Gwamnatin Edo za ta kirkiro da sabbin matakan hana yaduwar cutar zazzabin Lassa

0

Kwamishinan yada labarai na jihar Edo Paul Ohonbamu ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta kirkiro da hanyoyin da zai taimaka wajen hana yaduwar cutuka musamman cutar zazzabin Lassa a jihar.

Ohonbamu yace bisa ga abin da suka tattauna gwamnati ta amince ta hada hannu da masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya domin wayar da kan mutane kan hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

Ya ce gwamnatin ta kara amincewa kan ware Naira miliyan 600 domin inganta asibitin kula da mutanen da suka kamu da cutar zazzabin Lassa wanda ke Irrua sannan da Naira biliyan 1.4 domin ta amfana da shirin tsaftace muhalli wanda ake kira WASH wanda kungiyar kasashen turai EU da Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF suka shirya.

Daga karshe ya ce samun wannan shirin zai taimaka wajen hana bullowar cutuka a jihar.

Share.

game da Author