Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari ya bayyana cewa gwamnatin sa na goyan bayan kafa masana’antun sake sarrafa ledoji da tsoffin karafa a jihar.
Ya fadi haka ne yau Alhamis a lokacin da shugaban kamfanin sarrafa leda da tsoffin karafa dake Funtuwa ‘NAK Merchant Company’ Akilu Hassan ya ziyar ce shi a Katsina.
Hassan ya ziyar ci Masari ne domin samun goyan bayan sa kan sana’ar da suke yi sannan su roki gwamnati fili domin fadada masana’antan su.
Masari ya ce ya yi murna matuka ganin yadda matasan jihar ke samun aikin yi saboda bude wannan kamfani da akayi a jihar.
” Ina mai tabbatar muku da cewa gwamnati za tayi iya kokarin ta domin samar muku da filin da kuke bukata.
Daga karshe ya yi kira ga attajiran jihar su yi koyi da abin da Hassan ya yi wajen inganta rayuwar mutanen jihar.
Discussion about this post