Mataimakin Jam’iyyar PDP, tsohon Kakakin majalisa da wasu 34,826 sun koma APC

0

Mataimakin Jam’iyyar PDP a jihar Neja, Aminu Yusuf, tsohon kakakin majalisar,Adamu Usman, tsohon Antoni-janar na jihar, Abdullahi Wase da wasu ‘yan jam’iyyar 34,826 sun canza sheka zuwa APC.

Shugaban jam’iyyar John Oyegun da kan sa ya yayi tattaki zuwa Minna domin ya wa dubban masu canza sheka lale marhaban.

Oyegun ya bayyana musu cewa, jam’iyyar APC jam’iyya ce na talakawa da gyara kasa. ” Allah ne ya turo wa kasa Najeriya Buhari domin ya ceto ta daga halin da ta shiga.”

Bayan ayyukan gyara kasa da gwamnatin Buhari ke yi, ana ta kokarin ganin wutan lantarki ta wadata a ko-ina- a fadin kasar nan.

A karshe tsohon kakakin jihar, Adamu, ya ce sun dawo jam’iyyar APC ne domin su hada hannu da gwamnatin jihar domin ganin an sami ci gaba.

Share.

game da Author