Wasu ‘yan mata yara sun rasu a wata mota a Sabon garin Kano bayan sun shiga motar suna wasa inda garin haka kofar motar ta ki budewa kuma babu wanda ya iya jin ihun su sannan babu ta inda iska zai shiga cikin motar.
Ita dai wannan mota ta yi kusan shekara ta na ajiye a wannan wuri.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kano Magaji Majiya, ya ce daya daga cikin yan matan bata mutu sai dai rai kwa-kwai mutu kwa-kwai.
Yaran basu wuce shekaru hudu da haihuwa ba.