” Wani abin mamaki da ban takaici shine ganin yadda kasar nan ta fara zama abin wasan yara kanana.
” Da farko dai an ce beraye ne suka kori shugaban kasa daga ofishin sa, sannan aka ce maciji ya lunkume kudin hukumar JAMB, yanzu kuma an ce birai sun sace miliyan 70 a gonar sanata Adamu Abdullahi, cewar Sanata Shehu Sani.
Sanata Sani ya bayyana haka ne bayan tsige shugaban kungiyar sanatocin Arewa na majalisar dattawa, Sanata Adamu Abdullahi da akayi wa zargin wai ya waske da kudin kungiyar har naira miliyan 70.
Sanata Dino Melaye da shine kakakin kungiyar ya ce an sami matsala da shugaban kungiyar, wato Abdullahi Adamu tun bayan gazawa da yayi na gudanar da mulki kamar yadda ya kamata wa kungiyar.
” Kungiyar ta gaji miliyan 70 daga majalisar da ta gabata, amma babu bayanai kan yadda aka kashe su.”
Sai dai sanata Shehu Sani ya ce maganganun da ake ta yi a tsakanin su sanatoci shine wai birai ne suka far wa gonar Sanata Adamu inda suka waske da kudin kungiyar.
” Ni ba zan boye maganar ba, hakan shine ake ta rade-radi akai don haka kungiyar ta ga ya kamata ta canza shi.
An nada tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko a matsayin sabon shugaban kungiyar.
Discussion about this post