FAYOSE ZUWA GA BUHARI: ” Ka fara bayyana adadin kadarori da sunayen wadanda ke da su kafin ka saida”

0

Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose ya kalubalanci gwamnatin tarayya da ta bayyana adadin kadarorin da ta ce ta kwato daga wadanda su ka wawure dukiyar kasar nan, sannan kuma ta lissafa sunayen wadanda suka wawuri kadarorin kafin a sayar da su.

Fayose ya kara da cewa sannan kuma a daure a bayyana sunayen wadanda su ka sayi kadarorin idan an sayar.

Kakakin yada labaran gwamnan ne, Lere Olayinka ya fitar da wannan bayani daga bakin gwamnan, ya na mai cewa ‘yan Nijeriya sun fara gajiya da yadda ake jan akalar su a karkashin mulkin ‘yan farfaganda.

Fayose, wanda shi ne a sahun gaban sukar gwamnatin Muhammadu Buhari, ya yi wannan kalami ne biyo bayan jawabin da Buhari ya yi a Daura cewa, gwamnatin tarayya za ta saida kadarorin da aka kwato daga hannun wadanda su ka wawure dukiyar kasar nan.

Share.

game da Author