DON YA GOYI BAYAN BUHARI: Sanatocin Arewa sun sabule wa Sanata Abdullahi Adamu rigar mutunci

0

Sanatocin Arewa da ke karkashin Kungiyar Satocin Arewa, sun tsige shugaban kungiyar Sanata Abdullahi Adamu.

An maye gurbin sa da Sanata Aliyu Wammako, tsohon gwamnan jihar Sakoto.

Tsigewar da aka yi wa Adullahi Adamu, Sanata daga jIhar Nassarawa kuma tsohon gwamnan jihar, ta fito fili ne bayan da mataimakain shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu ya bayyana sanarwar a wani zama na yau Laraba.

“Wasikar tsige shi na dauke da sa hannun sakataren kungiyar, wanda Ya ce an cire Adamu ne sabooda zargin ya yi almubazzaranci da kudin kungiyar da kuma wasu laifukan da aka ce ya yi amma ba a bayyana su ba.

An tsige Adamu ne daidai lokacin da ya tayar da kura a kasar nan bayan majalisar ta amince da kudirin canza ranakun zabe, cewa su Saraki sun yi haka ne da muffin shirya wa Buhari gadar zare a zabe mai zuwa.

Share.

game da Author