Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin man fetur, Kabiru Marafa, ya kare Karamin Ministan Fetur, Ibe Kachikwu daga amsa wata tambaya mai sarkakiya.
A jiya ne Kachikwu ya gabatar a kan sa a gaban kwamitin, inda Sanata Isa Misau ya tambaye shi shin ko ya na samun damar ganawa da shuagaban kasa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, a matsayin sa na ministan fetur? Ko kuma shi Kachikwu bai iya ganin Buhari, sai dai ya aika da sako a kai masa kawai?
Sanata Misau ya kuma tambaye shi ko Shugaban Kasa ya san aikin da ya kamata ya yi kuma ya na yi yadda ya kamata a matsayin Shugaba Buhari na Ministan Fetur?
Sai dai kuma nan take Sanata Marafa, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya hana Kachikwu amsa wadannan tambayoyi, ya na mai nuni da cewa wadannan tambayoyi ba su shafi abin da kwamitin su ke bincika ba. Ya ce wannan magana ta shafi Kachikwu ne kadai ba ruwan ‘yan kwamiti da ita.
Marafa ya umarci Kachikwu kada ya masa tambayoyin, yayin da nan take ya yi shiru bai amsa su ba.
Sai dai kuma Kachikwu ya yi wani jirwaye mai kama da wanka, inda ya nuna cewa akwai wani taro da suka yi, wanda ya na sa rai nan gaba zai samu damar ganawa da shugaba Buhari nan ba da dadewa ba.