CAF: Mohammed Salah ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Afirka

0

Shahararren dan wasan kwallon kafa kasar Misra wato, Egypt, Mohammed Salah ne ya zama zakaran dan kwallon da yafi shahara a nahiyar Africa wannan shekara.

An sanar da haka ne yau, Alhamis, a bikin karrama ‘yan wasan kwallon kafa na CAF da aka yi.

Cikin wadanda suka yi takara a rukunin zama gwarzon shekarar sun hada da Sadio Mane dan wasan Liverpool na kasar Senegal da kuma dan kwallon kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang da yake kwallo a kungiyar Borussia Dortmund na kasar Jamus.

Asisat Oshoala, daga Najeriya ne ta lashe kyautar gwarzuwar shekara. Mai horas da ‘yan wasa na kasar masar Hector Cuper, shine ya lashe gwarzon mai horas da ‘yan wasa na shekara in da ita kanta kungiyar kwallon kafa ta kasar masar din ta lashe kyautar kungiyar da tafi shahara.

Share.

game da Author