KASHE-KASHE A BENUE: Buhari da APC ba su da tausayi, inji PDP

0

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa akwai tsananain rashin tausayi da Shugaba Muhammadu Buhari da kuma jam’iyyar APC mai mulki, ganin yadda ta bari ana ta kashe-kashe a kasar nan, musamman na baya-bayan nan da ya faru a jihar Benue.

Babbar jam’iyyar adawar ta ce kisan na Benue babban bala’i ne, kuma tsantsar keta ce matuka.

Yayin da ta ke ta’aziyya da kuma jaje ga iyalan wadanda aka kashe, PDP ta ce shugaban kasa da jam’iyyar sa mai mulki ba su da tausayi, kuma ba su dauki ran ’yan Najeriya a bakin komai ba.

A cikin wata takarda da sakataren yada labaran PDP na kasa baki daya, Kola Ologpdiyan ya sa wa hannu, ya ce da gwamnati mai yanzu ta san abin da ta ke yi, da tuni ta tabbatar da daukar matakan kauce wa wannan kashe-kashe da ya faru, musamman na Benue.

Kafin harin da aka kai na Benue, an bude wa wasu wuta a jihar Rivers, yayin da suke kan haryar su zuwa gida bayan sun halarci taron ibada a coci.

Sanan kuma a Kaduna an yi wani kashe-kashen a wasu kauyuka cikin karamar hukumar Sanga.

Rahotanni sun tabbatr da cewa an gudanar da zanga-zanga a Makurdi, sakamakon kisan da aka yi, wanda ake zargin Fulani makiyaya.

Share.

game da Author