Rundunar ‘Yan sandan Jihar Benue ta ce ta cafke wasu Fulani makiyaya takwas dangane da kisan da aka yi shekaranjiya a kuma jiya a jihar, a kananan hukumomin Guma da Logo.
Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar mai suna Moses Yamu ne ya bayyana haka a wani jawabi da ya tura wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya, NAN.
Ya ce an kama shida a Guma, biyu kuma a Logo. Kakakain ya ce a yanzu kurar ta kwanta tun bayan jami’an tsaro da aka jirke a yankunan, wadanda ke tabbatar da cewa ba a sake kai wani mummunan harin ba.
Gwamnan jihar ne da kansa ya bayyana cewa Fulani makiyaya sun kashe sama da mutane 20 a jihar. Rikici dai ya kara kamari inji gwamnan tun bayan kafa dokar haana kiwon dabbobi sakaka da jihar ta rattaba a ranar 1Ga Nuwamba, 2017.
Samuel Otom ya ce dokar na nan daram, ba za a cire ta ko a sassauta ta ba.
Bayan haka kuma mazauna garin Makurdi sun fito zanga-zanga a titunan garin don nuna fushin su ga ayyukan Fulani a yankunan jihar.
Wasu daga cikin masu zanga-zanga sun koka da yadda gwamnati tayi shiru kan kisan da fulani suke yi wa manoma a jihar.
Ruth Agba, ta ce suna da shaidun da ya nuna irin ta’adin da fulani suka yi wa mutanen jihar zuwa yanzu.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi tir da harin Fulanin ga mazauna kauyukan jihar Benue din, sannan ya bada umurnin a kara yawan jami’an tsaro zuwa yankunan kuma a tabbatar an kamo wadanda suka aikata wannan aiki.