A saka ranar 1 ga watan Muharram ranar hutu a Najeriya – Kungiyar ‘MURIC’

0

Kungiyar kare hakkin musulmai na Najeriya ‘MURIC’ karkashin shugabancin Ishaq Akintola ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saka da ranar daya ga watan Muharram ranar hutu kamar yadda daya ga watan Janairu yake ranar hutu.

Bisa ga bayanan takardar da ta fito daga ofishin shugaban kungiyar Akintola ya bayyana cewa hakan zai tabbatar wa musulman Najeriya cewa gwamnati na la’akari dasu cikin al’amuran ta.

Ya kuma ce kamata ya yi gwamanti ta tattauna da hukumar kula da al’amuran addinin musulunci ta Najeriya NSCIA domin tabbatar da ranar daya ga watan Muharram ya zama ranar hutu a kasar nan.

Daga karshe Ishaq ya ce idan aka yi haka kwanakin hutun da musulman kasan za su samu bisa ga kwanakin watan musulunci zai zama 4 sannan na addinin kirista zai zama biyar.

Share.

game da Author