Gobara ta babbake yara hudu a Zamfara

0

Mataimakin shugaban hukumar kashe gobara na jihar Zamfara Abdullahi Jibo ya bayyana cewa gobara ta babbake wasu yara hudu a kauyen Awala Filin- Jirgi a Gusau.

Ya ce gobarar ta tashi ne a gidan wani direba dake aiki a gidan gwamnatin a daren Talata.

” Mutanen kauyen sun kira mu a lokacin da gobarar ta fara da misalin karfe 10 na dare amma kafin mu isa wurin gobarar ta riga ta yi barnar da ta yi. Duk da haka sai da muka yi amfani da tankunan ruwa hudu.”

Jibo ya ce mai akwai yiwuwar matsalar da ake samu da wayoyin wutan lantarki ne ya yi sanadiyyar gobarar.
Sannan yayi kira ga mutane da su ci gaba da kiyaye sharuddan amfani da wutan lantarki domin kare kansu daga irin haka.

Yara maza biyu ne da mata biyu suka rasarayukan su a gobarar.

Share.

game da Author