APC za ta bai wa Igbo takarar Shugaban Kasa a 2023

0

Jam’iyyar APC mai mulki ta kamo hanyar damka wa dan kabilar Igbo takarar Shugaban Kasa a 2023. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kudu-maso-Gabas, Emma Eneukwu.

Eneukwu ya yi wanann furuci ne a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Ebonyi. Ya ce mafita ga ‘yan yankin Kudu-maso-Gabas kawai ita ce, su mara wa Shugaba Muhammadu Buhari baya a zaben 2019, domin yin haka ne zai sa APC ta damka takara ga dan kabilar Igbo a 2023, bayan kammala wa’adin Buhari.

A wurin taron, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya jaddada cewa kabilar Igbo za su bai wa jam’iyyar APC kashi 80% bisa 100% na kuri’u, domin a tabbatar da cewa APC ta yi nasara a 2019.

Sai dai kuma masu lura da al’amurran yadda siyasar Najeriya ke dagulewa idan zabe ya karato, su na ganin Kudu-maso-yamma ba za su amince a danka wa Igbo takara a karkashin jam’iyyar APC a 20123 ba. Ganin cewa Yemi Osinbajo da ke Mataimakin Shugaban Kasa a yanzu, shi ma ya na da damar tsayawa, kuma tabbas yankin Yarbawa za su goya masa baya.

Akwai kuma masu kallon cewa ankalin yankin Arewa zai fi karkata kuma zai fi kwanciya kawai idan aka damka takarar Shugabancin Kasa a karkashin APC a hannun Kudu-maso-yamma, ba kabilar Igbo ba, wadanda ke fitowa karaka su na nuna gaba ko tsanar yankin Arewa, musamman shi shugaba na yanzu Buhari, wanda su ka nemi yi wa tawaye a karkashin IPOB.

Share.

game da Author