2019: Kungiya mai zaman kanta ta tsaida Uba Sani don takarar Sanata a Kaduna

0

Wata kungiya mai suna Kaduna Democracy Monitors ta ce ta tsaida Malam Uba Sani a matsayin wanda ya cancanci yin takarar kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya a 2019.

A wata takarda ta musamman da kungiyar ta fitar bayan zaman ta, kakakin kungiyar Abdullahi Kwarbai ya ce Uba Sani ya cancanci yabo musamman ganin yadda ya jajurce wajen nuna adawar sa ga mulkin soji a kasar nan a wancan lokacin da yayi sanadiyyar dole suka hakura da mulkin.

” Irin halaye na Uba Sani da suka hada da girmama na gaba, yin siyasa ba da gaba ba da son jama’a ya sa muka ga babu wanda ya cancanci wannan kujera na sanata in ba shi ba a 2019.

Kungiyar ta ce ta gudanar zaben sanin rayoyin mazauna Kaduna ta tsakiya kuma abin da bayanai suka nuna bayan binciken sune, irin yadda mutane suke kara yin mubaya’a da Uba Sani da kuma kara kwanta musu a rai da ya ke yi.

” Yanzu fa duk wanda ya ke tunanin zai nemi wannan kujera, sai yayi da gaske zai iya samun kusa da kuri’un da Uba zai samu.”

Wasu daga cikin dalilan da ya sa Uba ya ke ta samun irin wadannan yabo daga jama’a kuma shine ganin irin shige da ficen da yayi a lokacin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari na ganin ya samu ruwan kuri’u a zaben.

Share.

game da Author