Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a cikin sabuwar shekaran nan ta 2018 ne Gwamnatin Tarayya za ta haramta shigo da shinkafa daga kasashen waje.
A cikin jawabin sa na Sabuwar Shekara, Buhari ya ce an tabbatar da an samu yalwar noma kuma damina ta yi albarka a 2017, an kuma samu abinci sosai.
Ya ce babu wani alfanu na ci gaba da kashe bilyoyin nairori a kullum ana shigo da abin da ‘yan kasar nan ke nomawa ko su ke iya nomawa.
Shugaban ya kara nanata cewa gwamnatin sa na kan hanyar ta wajen tabbatar da saisaita alkiblar kasar nan, ya na mai cewa ‘yan Nijeriya na bukatar ganin an magance wasu matsaloli a cikin gaggawa, ko sha-yanzu-magani-yanzu.
Ya ce amma wasu matsalolin sun dade shekara da shekaru su na ruruwa a kasar nan, zai yi wahala a warware su farat daya, sai a hankali.
Tun da farkon jawabin sa, Buhari ya fara ne da bai wa ‘yan Nijeriya hakurin wahalar da su ka tsinci kan su a lokacin shagulgulan Kirsimeti, ta matsalar karanci da tsadar man fetur. Ya ce wasu batagari ne su ka haddasa matsalar, kuma ba zai yiwu su ci bulus ba, sai an gano su, an hukunta su.
Da ya juya kan bukatar zaman lafiya, ya yi tsokacin cewa zaman lafiya tare da juna duk da bambancin addini da yawan kabilu shi ne mafi alkairi ga kasar nan. Sai ya jinjina kuma ya buga misali da yankin Kudu-maso-yamma na Yarbawa, inda Buhari ya ce duk da bambancin addinin da ke tsakanin su, sun dinke kan su a wuri daya ba tare da nuna bambanci ko yawan tashin-tashina ba.