David Mark ya ragargaji EFCC

0

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Davida Mark, ya ragargaji Hukumar EFCC, ya na mai cewa sun kirkiri karya da kazafi mara dalili sun sagala masa a wuya.

Mark ya yi wannan bayani ne bayan ya fito daga ofishin EFCC, inda aka shafe lokaci mai tsawo ana yi masa ruwan tambayoyi.

Sanata Mark, ya fusata ne dangane da abinda ya kira zargin badakala da harkallar da aka yi masa, wadda yace ba shi da masaniya kan maganar.

A wani bayani da jami’in hulda da jama’a na Mark, mai suna Paul Mumeh ya sa wa hannu ranar Lahadi, ya tabbatar da cewa sanatan ya kai kansa ofishin EFCC kan wata gayyata da su ka yi masa, dangane da batun harkallar wasu kudin kamfen da aka ce da hannun sa aka yi ta a cikin 2015, a jihar Benue,

Amma abin da ya fi bata masa rai shi ne wata tambaya a aka yi masa dangane da korafin wata toshiyar baki ta makudan kudade wai an bai wa dukkan mambobin majalisar tarayya, cikin 2010.

David Mark dai shi ne Shugaban Majalisar Tarayya tsakanin 2007 zuwa 2015.

Ya ce EFCC sun tambaye shi cewa PDP ta kimshe tsabar kudi har naira biliyan 2 a cikin asusun ajiyar banki mallakar Majalisar Tarayya.

Daga nan kuma ya kara da cewa EFCC ta yi zargin cewa an raba kudin tsakanin dukkan mambobin Majalisar Dattijai 109, da su ka hada da na PDP, ANPP da ACN a cikin 2010.

Kakakin yada labaran Mark, ya kara da cewa Mark ya ce bai ga dalilin da zai sa PDP ta kwashi kudi, ta zuba asusun Majalisar Tarayya ba. Idan ma akwai dalilin, to ba a yi haka a zamanin sa Sanata Mark ba.

EFCC ba su maida martanin wadannan kalamai na David Mark ba.

Share.

game da Author