Wata sabuwar amarya Basakkwaciya, mai suna Shafa Muhammad, ta tsatsatsala wa angon ta sabuwar reza a kai, inda ta ji masa ciwo.
Shafa mai shekaru 28 da haihuwa, ita da mijin su na zaune ne a kauyen Akillar Liman, cikin Karamar Hukumar Wamakko da ke jihar Sokoto.
Wannan mummunan al’amari ya faru ne a ranar 16 Ga Disamba, mako uku kadai bayan tarewar amarya. Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito cewa tun farko auren-dole ne aka yi wa Shafa tare da Umar Shehu, ba da son ran ta ba.
“Mijin ya shiga cikin daki ya na mai dokin ya kwanta da amaryar sa, sai kawai ta rarume shi, ta yi ta tsala masa reza a kai.
“Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan Sokoto, Ibrahim Abarass, ya ce an yi wa mijin magani, kuma har an sallame shi daga asibiti, ya koma gida.
Ya shawarci iyaye da su daina yi wa ‘ya’yan su auren-dole.
Ya ce tuni an cafke amaryar, kuma ana shirin gurfanar da ita a gaban alkali.