Tabbas zan fi Buhari tabukawa Idan da nine shugaban Kasa

0

Shahararren mawakin nan, Majek Fashek ya bayyana cewa Idan da shine shugaban Kasa sai ya fi Buhari yin aiki wa ‘yan Najeriya.

” Babu abin da zai sa no ban fi Buhari tabuka abin azo a gani ba. Mutanen Najeriya na matukar shan dan Karan wahala a kasar nan.

” Kamfanoni sai tattara nasu-ina-su suke yi suna fice da ga kasar nan sannan ‘yan Najeriya na fama da matsanancin talauci Kuma wai ace ana da gwamnati.

” Idan dai Kai ba dan majalisa bane ko Sanata ko Kuma mahaifinka ba babban jami’in gwamnati bane to ka kade. Domin wahala salamu Alaikum. Zaka ga mata kanana a titunan kasar nan suna karuwanci duk domin neman abin da za sa a ciki.

Majek Fashek ya na shirin sako sabuwar wakar sa nan ba da dadewa ba.

Share.

game da Author