Uwargidan tsohon shugaban jam’iyyar APC ta koma Mariam Ali ta canza sheka zuwa jam’iyyar APC daga PDP.
Mariam Ali dai ta rike mukamai masu girma a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Sannan ta ce tayi haka ne don kashin kan ta duk da cewa mijin ta shine wanda yafi dadewa a kujeran shugabancin jam’iyyar PDP.
” Mijina Musulmi ne dan Arewa, ni kuma Kirista ce yar Kudu-Maso-Kudu. Abin da nayi ya nuna hadin kan kasa ne da kuma neman ci gaba da yi wa kasa aiki.”
Shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun ne ya karbi Mariam Ali a ofishin Jam’iyyar dake Abuja.