SUN SATA AN SACE: Yadda aka yi watandar gidaje 222 da Maina ya kwato

0

Binciken da Kwamitin Majalisar Dattawa ke yi dangane da badakalar maida tsohon shugaban Hukumar Fansho kan aikin sa a asirce ya dauki sabon salo a yau Alhamis.

Kwamitin na Majalisar Dattawa wanda ke binciken yadda aka maida Maina kan aiki, a yau Alhamis ya bayyana cewa kwamitin Maina ya kwato gidaje 222 da kadarori daga hannun wasu da suka danne kudaden fansho a Abuja da wasu manyan biranen kasar nan.

Kwamitin kuma ya nemi a kara masa lokacin yin binciken da ya ke a kan yi yanzu.

Shugaban Kwamitin Emmanual Paulker, Sanatan PDP daga jihar Delta, ya ce kwamitin sa ya kasa gabatar da da rahoton sa saboda cukumurda da sarkakiyar da ke tattare da rikicin Maina, domin a zaman yanzu ma sun ci karo da wata harkalla da aka lunke a baibai a can baya.

Ya ce an gano wasu bayanai wadanda sun shige karfin ikon da aka ba kwamitin, wadanda tilas sai dai Majalisa ce da kan ta za ta yi aiki a kan su.

“Yayin da muke gudanar da bincike, mun gano cewa akwai wasu manyan rukunin gidaje da Maina ya bankado a lokacin da ya ke yin nasa binciken harkallar cin kudaden fansho.

Daga cikin su ya ce akwai gidaje har 222 da wasu kadarori da Maina ya bankado a Abuja da wasu garuruwa.

“Aikin da Maina ya yi tare da EFCC, ICPC, DSS, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro ne suka gano wadannan makudan kadarorin.

“Sai dai kuma wadannan tulin kadarorin da Maiana ya bankado, duk wasu tsiraru ne suka rabas da su a tsakanin su.

Kwamitin mu kuma ya karbi wasu korafe-korafe a kan wadannan kadarori da aka rabas.

A yau ne dai aka tsara Maina da dukkan wadanda aka zarga da hannu wajen dawo da shi kan aiki a asircr za su bayyana a gaban Majalisar Tarayya.

Yayin da Maina bai halarta ba, Ministan Shari’a Abubakar Malami ya shaida wa Majalisa cewa zargin da ke yi masa shi ne ya rubuta takardar maida Maina a wurin aiki ba gaskiya ba ne.

Majalisa dai ta kara wa kwamitin bincike wa’adin wata daya domin ta kammala komai a kan lokaci.

Idan ba a manta ba, an kori Maina a cikin 2013. Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ce ta kore shi, sakamakon wata takardar da Shugaban Ma’aikata na lokacin ya rubuta ya na neman a kore shi, a bisa zargin harkallar biliyoyin kudaden fansho.

Cikin 2012 ne dai aka zargi Maina da yin harkalla har ta naira bilyan 100. A cikin 2010 ne gwamnatin Goodluck Jonathan ta nada shi ya tsarkake harkar biyan kudin fansho.

Daga zargin da aka yi masa ne Majalisar Dattawa ta gayyace shi. Daga nan ta umarci a gagauta kama shi. Shi kuma Maina sai ya maka Majalisar Dattawa kotu, tare da Sufeto Janar na ‘Yan sanda na lokacin MD Abubakar, kuma ya shiga wasan buya.

An kai karar su a kotu a ranar 21 Ga Yuli, 2015 tare da Stephen Oronsaye. An caje su da aikata laifuka na harkalla har 24. Sauran sun bayyana a kotu, amma shi Maina ya tsere.

An ce Maina ya shafe shekaru a Dubai, inda daga can ya rika kamun-kafa a cikin gwamnatin Buhari domin a maida shi kan mukamin sa.

Share.

game da Author