Gamayyar kungiyoyin matasan arewacin Najeriya sun yaba wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan amai da hankali da yai wajen ganin yaki da cin hanci da rashawa da ya sa a gaba ya samu nasara.
Kungiyoyin da suka sanar da haka bayan taro da suka yi a Kaduna sun jinjina wa shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu kan kokari da yake yi wajen ganin ba an samu nasara a yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatin Buhari ke yi.
Shugaban wannan gamayya na kungiyoyi, kuma shugaban kungiyar Arewa Transparency Champions, ATC, Bashir Ibrahim ya kara da cewa dole ne fa a yaba wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari da shugaban hukumar EFCC, Magu kan irin rawar da suka taka wajen seta kasar nan kan tafarkin gaskiya da rikon amana kamar yadda suka yi alkawari a lokacin Kamfen din 2015.
Bayan haka kuma kungiyoyin sun ce za su shirya gangami na mutane miliyan daya domin nuna goyon bayan su ga Buhari.
Sauran kungiyoyin da suka halarci taron sun hada da Daniel Magaji na Northern Accountability Front, Hadiza Bukar na Arewa Gender Promotion Campaign, Sani Idris na United Front Against Corrupt Practices da Reuben Magaji of Youth for Transparency Initiative.
Discussion about this post