Jim kadan bayan PREMIUM TIMES HAUSA da PREMIUM TIMES sun buga hirar da jaridar ta yi da Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, SULE LAMIDO, a jiya da dare da kuma yau da safe, jama’a na ci gaba da bayyana ra’ayoyin su dangane da abin da su ka karanta a tattaunawar.
Ga wasu muhimman batutuwa 10 da Lamido ya yi magana a kan su, wadanda za a iya cewa su suka sa ake ta sharhin bayanan da Lamido ya yi. Watakila saboda alamomi na nuni da cewa zaben 2019 mai zuwa, Fulani ne guda biyu za su kafsa a tsakanin su, domin takarar kujerar da Buhari ya ke a kai. Hausawa dai na cewa ‘gwangwa-da-gwangwa gadar giwa, dan rakumi tsaya ka yi kallo:
1 – APC BA ZA TA IYA HADA KAN NAJERIYA BA
“Watau idan aka yi duba da irin yadda al’amarin kasar nan ke tafiya, jam’iyyar APC fa ba za ta iya hada kan Nijeriya ba. Ba wai adawa ce na ke kokarin nunawa ba, amma idan ka yi nazarin abin da ke faruwa a Nijeriya daga shekaru uku zuwa yau, za ka kara fahimtar cewa akwai damuwa a zukatan ‘yan Nijeriya.”
2 – APC SHEKAR TSUNTSAYE CE
“To, yanzu da su ka koma can, me aka tsinana musu? Sun samu kwanciyar hankali? An yi musu sakayya? Sun tsira daga abin da su ke gudu? Idan sun dawo, to dama ba sabon abu ba ne, sun dawo cikin jam’iyyar da su ka bari. Dama ai PDP ce gidan su, amma APC ai gidan haya ce ko shekar tsuntsaye, ba gidan zama ba ce. Shi gidan haya kuwa zaman a-taru-a-kwana ake yi, ba zaman-dirshan ba.”
“Tun daga Atiku da Saraki da ma kowane a cikin su duk mu na yi musu lale marhabin idan su ka dawo. Dama na mu ne, ‘yan PDP, duk inda su ka shiga, to akwai jinin PDP a jikin su. Duk nisan gudun da mutum zai yi, ai ba zai iya tsere wa ran sa ba. Dangane da batun kafa sharuddan dawowar Atiku kuwa, ba na jin akwai wasu sharudda. To wane ne ya gindaya sharuddan? Yaushe aka gindaya su? Kai, babu wasu sharudda. Idan sun dawo dai za mu karbe su hannu bibbiyu, tunda za su dawo inda su ka fi kauna, inda aka fi daukar su da daraja da mutunci, kuma inda su ka zama yadda su ke a yau.
3 – YADDA APC KE TOZARTA ’YAN PDPin DA KE CIKIN TA
“Amma a halin da su ke yanzu, kowa ya san sun zama mujiya a cikin tsuntsaye. Yau a ci mutuncin su, gobe tozarta su, jibi a ce musu barayi. A ce PDP jam’iyyar barayi a gaban su, kuma ba su iya tankawa ko su kare kan su. An jima ka ji Lai ya ce ba su da kunya, kuma su na kallo ana yi musu wannan cin-fuska.
4 – PDP CE TA KAFA GWAMNATIN BUHARI
“To su je su yi ta jifar mu da kowane irin mummunan kalami. Abin da kowa ya sani dai shi ne, PDP ce ta kafa gwamnatin APC. Gwamnatin APC dai ta mu ce mu ‘yan PDP.
5 – APC BA TA SHIRYA KARBAR MULKI BA
“Wato ka lura da wani abu, a matsayina na dan Nijeriya, a gaskiya ba na murna da irin shirmen da gwamnatin Buhari ke tafkawa. Ko na ce gwamnatin APC. An ba su nauyin jagorancin jama’a, amma abin bakin ciki kawai shi ne, sun samu mulki da rana tsaka, alhali ba su shirya ba, kuma ba su da wani shiri a lokacin.
“Saboda ba su shirya ba fa shi ya sa su ke biye su na shirga karairayi domin su lullube shirmen da su ke tafkawa. A lokacin da su ke kamfen, ba su komai sai jifar PDP da kazafin cewa ita ce Boko Haram, sun yi ta ce mana shaidanu, su na muzanta mu. To a yanzu da gwamnati ke hannun su, sun kasa farkawa daga barcin tunanin cewa har yanzu dabi’un su na ‘yan adawa ne masu neman mulki, sun kasa gane cewa a yansu mulkin a hannun su ya ke.
“Saboda fa kwakwalwar su a toshe ta ke, ba su kuma da sanin makamar-akalar-gwamnati, sai su ke ta yada farfaganda daya. Sannan kuma idan ka yi magana a kan wani shirme da bulkarar da gwamnatin su ke tabkawa, a matsayin ka na dan Najeriya, sai su rika muzanta ka. Ka ga akwai hadari a ce gwamnati ce ke muzanta dan Nijeriya idan ya koka dangane da ita.
6 – GWASALE MASU KUKA DA GWAMNATIN BUHARI
“Yau a Najeriya sai mutanen gwamnati su rika muzanta ‘yan Najeriya, idan su ka bayyana ra’ayin su dangane da yadda gwamnati ke nunke su baibai. Idan ka yi korafi sai su ce maka sarkin korafi. To wai idan ka na korafi dangane da abin da aka yi maka na ba daidai ba, kamata ya yi gwamnati ta tambaye ka, me ya sa ka ke raki. Maimakon haka, sai a fara shaguben ka ana cewa sarkin raki.
“Shin idan ‘ya’yan ka na kuka saboda su a jin yunwa, ya za ka yi da su? Za ka fita ka nemo musu abainci ne, ko kuwa za ka rika yi musu fada ka na cewa sun cika raki?
7 – GWAMNATIN MAKARYATA
“Ka duba ka gani, lokacin da Shugaba Buhari ba shi da lafiya har aka tafi da shi waje, sai Lai da Adesina su ka rika cewa wai ya na dai can kwance ne ya na shan magunguna kawai. Amma lafiyar sa kalau. Amma lokacin da ya dawo, sai ya ce ai ya sha fama da rashin lafiya. To mene ne abin boyewa ga rashin lafiya? Buharin nan fa ba na Lai ko Adesina kadai ba ne su biyu.
“Lokacin da ‘Yar’Adua ba shi da lafiya, su Lai ne fa a sahun gaban masu cewa sai an bayyana rashin lafiyar sa. Har cewa su ke yi su na da ‘yancin su san hatta yadda shugaban kasa ke shan ruwa. To yanzu ga su rike da ragamar shugabanci, mu na ta shan mamakin irin tulin karairayin da su ke kantara mana.
8 – YAWAITAR MASU RAKI
“Aka zo aka ce Asibitin Fadar Shuagaban Kasa babu ko sirinji. Matar shugaban kasa ce da kan ta ta fadi haka fa, bayan an ce an ware masa kasafin naira bilyan uku. Maimakon su gaggauta kai magani, sai aka rika cewa mun cika raki. To Alhadu Lillahi, a yau har Aisha na cikin masu raki da kukan cewa ana ba daidai ba a gwamnatin Buhari. Ita kan ta APC din ta fara raki. Ka ga Nijeriya ta zama kasar masu raki kenan.
9 – MASU ZUBA JARI NA GUDUN NAJERIYA
“Amma mu kuma a nan, wannan gwamnati wacce idan ta yi ba daidai ba ka yi magana sai ta ce ka cika raki, gwamnatin da ta raba kan ‘yan Nijeriya, ba s da wani tunani ko basirar iya fidda kitse daga wuta. A cikin shekara biyu da rabi da su ka gabata zuwa yau, kamfanoni nawa ne daga kasashen waje su ka shigo Nijeiya su ka zuba wani abin kirki da sunan jari a cikin kasar nan? Babu! Ta yaya za su iya tabuka wani abin kirki? Ku dubi Angola kuma ku dubi yadda ake zuba dimbin jari a cikin kasar. Ga Masar nan a yanzu ta na bugun gaba da tinkaho da karfin tattalin arzikin ta. Ga kuma kananan kasashe irin su Rwanda. Don haka duk yadda z aka cika mutane da surutai da dadin zance, idan ba ka da basira fa ba za ka iya saisaita Nijeriya a kan turba ba.
“Ita fa kwakwalwar dan Adam dama can an yi ta ne domin ta tunkari kalubale. Na ga kasashe da yawa wadanda ba su da komai a da can, daga baya kuma sun zama hamshakai. Abin fa ya dogara ne, ga kyakkywan tunanin bullo da hanyoyi mafita. Ba wai kawai surutai ba ne abin ko wani kame-kame. Kasashe da dama ba su da kayan kera abubuwa, babu albarkatun kasa, amma sun kokarta sun zama manyan kasashen da ake tutiya da su a yau. Ai sai ka na da basirar yin tunanin kawo ci gaba sannan za ka iya ci gaba.
Ga Koriya ta Kudu nan, su ne a sahun gaban kasashe masu gina manyan jiragen ruwa, amma kuma ba su da kayan hadin kera jiragen ruwa a kasar su.
10 – NA KA SHI KE BADA KAI
“Nan aka wayi gari daya daga cikin mashawartan Buhari mai suna Farfesa Itse Sagey ya ce jam’iyyar APC garken barayi ce, garken mahandama ce. Kuma ya na cikin gwamnatin ta APC. Shin ta yaya masu zuba jari daga kasashen waje za su amince su shigo su zuba jari a Najeriya?”