TAMBAYA: Assalamu alaikum Waraumatullah, Allah ya gafarta ma malam ya kara mishi basira, malam ina da tambaya kamar haka, Annabi Muhammad SAW ya taba azumtar goman farkon dhulhijja gaba daya?
AMSA: Amin, Allah ya karbi Idadar mu, Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
AZUMIN KWANAKI GOMAN FARKON DHUL-HIJJA
Azumin kwana taran Dhul-Hajji tare da kamun bakin ranar Sallah zuwa sauka idi, yana daga cikin jerin ayyuka kyawawa a cikin kwanaki goman Dhul-Hahhi. Hadisi ya inganta acikin falalar goman Dhul_Hajji, cewa babu wani aikin kwarai da ya fi soyowa ga Allah fiye da aikin alkhairi a cikin goman Dhul_Hajji. Sabo da girman falalar azumi kuma, Allah yace: azumi nawa ne, kuma ni ne mai biyan sakamakon sa.
Annabin tsira (SAW) ya kwadaitar da yin kyawawan ayyuka a cikin wadannan kwanaki goman Dhul_Hajji masu daraja, azumi daya ne daga cikin mafi girman ibadan da shi Annabi SAW ya yi a cikin kwanakin.
Lallai an rowaito a ckin ingattacen Hadisi cewa Annabin tsira (SAW) yana azumtar goman farkon Dhul-Hajji gaba daya. Ga hadisin Kamar Haka:
An karbo daga Hudaidatu dan Khalid daga matarsa, ta karbo daga sashin matan Annabi (SAW) sunce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana azumtar Kwanaki taran Dhul-Hajji, da ranar Ashura, da kwanaki uku a kowane wata …” Imam Abu-Dauda ya ruwaito Hadisin, a cikin Sunan, Lambar Hadisi 2437 (1/741), Imamu Baihaqi ya ruwaito Hadisin, a cikin Sunanul-Kubrah, Lambar Hadisi 8176 , Imam Al-Nisa’i ma ya ruwaito Hadisin, a cikin Alkubrah, Lambar Hadisi 2726 (2/135). Malam Nasiru-Din Albani yace Hadisin SAHIHI ne ( wa to, ingattacen Hadisi).
Imam An-Nawawi da sauran manyan malamai kamar Iban Hajar, Attahawi, Shawkani, Suyuti, da manyan limaman duniyar Malikiyya, Shafi’iyya, Hanafiyya, Hambaliyya, Zahiriyya, duk sunce azumtar wadannan kwanakin sunna ne.
Babu sabani a cikin abinda nasani cewa ana azumtar goman farkon Dhul-Hajji, ga mai son yin hakan. Allah shi ne mafi sani.
Yallah Ka bamu lafiya da abinda lafiyar zata ci. Amin.
Discussion about this post