Hukumar NAFDAC ta maka shugaban kamfanin ‘Tasty Time’ a kotu

0

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta maka kamfanin‘Tasty Time Nigeria Ltd da shugaban ta Isaac Kole a kotu a Legas saboda kama kamfanin da laifin sarrafa jabun lemun zaki da rashin yi musu rijista da hukumar.

Alkalin kotun Hadiza Rabiu-Shagari ta ba Kole damar neman beli duk da cewa bai amince da laifin da ake zargin sa ba.

Alkalin ta daga sauraron karan zuwa 6 ga watan Nuwamba.

Share.

game da Author