Ministan Ilimi ya nemi Buhari ya kara yawan kudade a fannin ilimi

0

An ja hankalin Shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa dokar-ta-baci a fannin ilimi, tare da kara yawan kudaden da gwamnati ke kashewa a fannin na ilimi.

Ministan Ilmi Adamu Adamu ne da kan sa ya yi wannan kiran a ranar Litinin yayin da ya ke jawabi a taron da fadar shugaban kasa ta shirya wa ministoci kan harkokin ilimi.

A ta bakin Adamu, ya roki Shugaba Buhari ya kara maida hankali matuka ainun a fannin ilimi, kamar yadda ya maida hankali kan matsalar rashin tsaro da kuma inganta tattalin arzi.

Ya kara da cewa a gaskiya kudaden da Najeriya ke kshewa a fannin ilimi ba su taka kara sun karya ba, idan aka kwatanta da wasu kananan kasashe na yankin Saharar Afrika. Adamu ya kuma yi gargadin cewa gwamnatin tarayya sai fa ta kara kashe kudade a fannin ilimi idan har ana so a ga canji.

Da ya ci gaba da bayani, sai ministan ya ce idan har shugaban kasa na bukatar cika alkawurra 13 da ya daukar wa Najeriya lokacin zabe a kan inganta ilimi, to tilas sai an rika kashe akalla naira tirilyan daya a duk shekara a fannin ilimi.

Idan ba a manta ba, Shugaba Muhammadu Buhari ya ware naira bilyan 605.8 da za a kashe a fannin ilimi, wato kashi 6 bisa 100 kacal na kasasfin 2018.

Share.

game da Author