PDP ta kafa kwamitin karbar masu canja sheka

0

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta kafa kwamiti da zai tattauna da dawo da wadanda suka bar jam’iyyar zuwa wata jam’iyyun kasar nan.

Kamar yadda shugaban jam’iyyar, Hassan Hyat ya bayana, za kuma a yi kokarin dawo da wasu cikin jam’iyyar.

Hyat ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN a Jos cewa kowace mazabar Sanata na da kwamiti wadanda aka dora masa nauyin dawo da wasu ‘yan jam’iyyar zuwa cikin PDP.

‘Har an kammala bayar da bayanin rahotan daya daga cikin shiyyar sanatocin uku.”

Ya kara da cewa akwai ma wasu jiga-jigan PDP da suka canja sheka shekaru biyu da suka gabata, amma yanzu sun dawo PDP.

“Daga cikin su akwai tsoffin kwamishinoni, ’yan majalisar jiha da shugabannin kananan hukumomi; kuma kofar mu a bude ta ke ga duk masu son dawowa gidan su ana ainihi, PDP.”

Share.

game da Author