ASARKALA: Yadda Dangote ya kimshe kudi a waje don kauce wa biyan haraji

0

Binciken kwakwaf da a duniya ya bayyana bayan an fallasa, wanda aka fi sani da Paradise Papers, ya tabbatar da cewa Babban hamshakin attajirin da duk Afrika babu kamar sa, Aliko Dangote, ya kimshe makudan kudaden sa a kasashen waje, da nufin kauce wa biyan haraji.

Wasu takardun bayanai na sirri da wani kamfanin tattara bayanai na Panama, Mossack Fonseca, tun a cikin 2016 ya alakanta Dangote da dan’uwan sa Dantata, su na da akalla kamfanoni har 13 a Tsibirin Seychelles, wadanda ake kimshe kudade da sunan su.

Dama kuma a baya can cikin 2015, PREMIUM TIMES tare da hadin guiwa da wata jarida ta kasar Faransa, mai suna La Monde, sun fallasa Dangote cewa ya na daya daga cikin masu asusun ajiya na sirri a wani reshen bankin HSBC da ke Swissland.

Ana wata kuma sai ga wata, wani sabon bincike ya sake nuna cewa Dangote ya yi kimshen zunzurutun dalar Amurka har bilyan 5.8 a wani kamfani mai suna Greenview International Corp., da ke Cayman, kamar yadda Premium Times ta binciko.

Ana dai kyasta cewa Dangote na da arzikin da ya kai dalar Amurka biliyan 12.1.

Wasu tulin takardun bayanai da suka fado hannun PREMIUM TIMES, wadanda daga cikin kunshin bayanan Appleby ne Paradise Papers ta bayyana su, sun nuna cewa Dangote na da kudi a kamfanin Greenview tun a 1994.

Bayanan sun kara nuna cewa wani mai suna Vernon Emmauel shi ne shugaban kamfanin, yayin da Dlio Mela da LiliaTover De Leon na daya daga cikin daraktocin kamfanin. Yawancin wadanda ake nadawa a matsayin shugabanni, duk na je-ka-na-yi-ka ne, kuma mazauna yankunan da aka kafa kamfanonin ne.

An kuma gano cewa dukkan daraktocin uku sun ajiye mukaman su a ranar da Dangote ya zama Babban Darakta kuma mai hannayen jarin kamfanin a ranar 24 Ga Agusta, 2015.

Wani bincike kuma ya nuna wasu bayanan kididdiga da Dangote ya sa wa hannu a cikin 2013, a madadin Greenview shi da babban jami’in kula da harkokinn kudi na Dangote Industries Limited mai suna Mustapha Ibrahim da kuma wani babban jami’i mai suna Kunle Alake, sun tabbatar da cewa ya zuwa Janairu 2012, hannun jarinn Dangote a kamfanin ya kai Dala Bilyan 3. Amma kuma ya zuwa Disamba, 2013, sai ga shi hannun jarin ya nunka zuwa Dala Bilyan 5.8.

Premium Times ta tuntubi Mista Alake a Lagos, wanda ya yi magana a madadin Dangote. Yace Greenview ba kamfanin kimshe kudi ba ne, kamfani ne mai tafiyar da wasu harkokin kasuwancin Dangote.

Share.

game da Author