Buhari ne ya umurci ministan Shari’a ya tattauna da ni sannan ya tabbata an dawo dani aiki – Inji Maina

0

AbdulRasheed Maina ya ce maganar dawo da shi aiki ya samo asali ne tun bayan ganawa da suka yi da ministan shari’a Abubakar Malami wanda Buhari ne da kan sa ya sa ministan yayi zam dashi.

Maina ya fadi haka ne da yake hira da gidan Talabijin din Channels.

“ Na kai karar duka hukumomin tsaron da suke Magana akai kuma na samu nasara akan su a kotu.

“ Bayan wannan gwamnati ta zauna da ni mun tattauna sai nace musu ba zan bar su su koma gida haka nan kawai ba zan dan basu wani abu su sa a aljihu. Sai ministan shari’a ya ce me nene ko zan basu ? sai na basu wasu takardun sirri da ya nuna yadda ake satan kudin fansho a kasar nan sannan na ce masa takardun na bayanin wasu kudade ne da za a sace da ya kai naira Tiriliya 1.3. Na ce masa kuje maza-maza domin wasu zasu sace su, Haka suke yi duk shekara. Na ce masa ya koma Najeriya ya bi diddigin wannan magana da nake yi tare da wannan takardu da na basa zai tabbatar da abin da nake fadi.

“ Ba zan ce hannu na a wanke suke ba amma fa na yi iya kokarina domin na kawo gyara a aikin. Da minista Malami ya dawo Najeriya sai ya ce lallai na bashi bayanan gaske, ya tambaye ni yashe zan dawo. Ni kuma na ce masa akwai dokar kotu a kaina saboda haka minista ya duba ya ce dole abi wannan hukunci na kotu da ta yanke akai nan a mai da ni aikin na.”

Maina ya ce shi dai mai gaskiya ne, kuma yana rokon Buhari ya bashi dama su zauna domin tona ma barayin kudaden Fansho asiri.

Share.

game da Author