Askarawan Najeriya sun ceto mutane 30 da Boko Haram ta yi garkuwa da su

0

Dakarun sojin Najeriya da jami’an tsaro na ‘Mobile Strike Team MST’ sun kashe ‘yan Boko Haram 14 sannan sun ceto wasu mutane da suka yi garkuwa dasu su 30.

Kakakin rundunar sojin Najeriya Sani Usman ne ya sanar da haka ranar Talata a jihar Borno.

Ya ce askarawan sun yi arangama da ‘yan Boko Haram a wasu kauyukan karamar hukumar Bama da ya hada da Abusuriwa, Newchina, Bonzon, Usmanari, Goyayeri, Shitimari, Gashimari da Awaram kuma sun sami nasaran kwato ceto wadanda suka yi garkuwa da su.

“Mun kwato maza uku, mata 12, wanda daga cikin su akwai tsoho daya da tsohuwa daya da yara 15 sannan mun kwato bindigogi da harsasai da yawa a hannun su.”

Share.

game da Author