Hukumomin Yaki Da Rashawa sun kasa bayyana dukiyar da suka kwato -Saraki

1

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa har yau an kasa samun cikakken bayanin ba’asin inda wasu tulin kudaden da hukumomin hana cin hanci da rashawa suka kwato.

Yay i wannan bayani ne a wurin wani taron da ya jibinci dokar hana cin hanci da rashawa a Majalisar Tarayya.

Saraki ya ce saboda jami’an hana rashawa sun kasa bayyana inda wasu kudaden da suka kwato suke, ko yadda aka yi da su, dalili kenan wasu kasashe da yawa ba su daukar yaki da cin hancin da Najeriya ke yi da wani muhimmanci.

“Dalili fa kenan Najeriya ke kasa gamsar da kasashen da ke son dawo mata da dukiyar da aka sace ke kaffa-kaffa da maida wa Najeriya kudaden, domin su na ganin kamar ja-ya-fado-ja-ya-dauka kawai ake yi.

“Ku na dai gani kwanan nan Shugaban Kasa ya kafa kwamitin da zai bi kadi tare da tantance yawan dukiyar da hukumomin hana cin hanci suka kwato.” Inji Saraki.

Share.

game da Author