Yadda Buhari Ya Haddasa Harkallar NNPC

0

Rashin jituwar da ta kamre tsakanin Karamin Ministan Man Fetur, Ibe Kachikwu da Shugaban Kamfanin NNPC, Maikanti Baru, ta yi tsami sosai har sun fara kwance wa juna wando a tsakiyar kasuwa.

Yayin da wasu ke ganin cewa Kachikwu ne ke neman cukuikuye Baru a barranta shi daga NNPC, wasu kuma na ganin cewa Baru ne ya barranta kan sa daga Ogan sa Kachikwu, har ya kai ga ya daburta ka’idojin bayar da kwangiloli a NNPC.

Jaridar PREMIUM TIMES HAUSA ta bi diddigin sabanin har zuwa yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi sakacin da sabanin ya kai ga zama harkalla.

RANAR 30 GA AGUSTA:

Wannan babbar matsala dai ita ce ta yi sanadiyyar hasalar Karamin Ministan Man Fetur, Ibe Kachikwu, har ya fusata ya rubuta wa Shuagaban Kasa wasika, inda a ciki ya yi korafin cewa Shugaban NNPC Maikanti Baru cewa ya na yin gaban kan sa a wajen aiwatarwa ko gudanar da wasu ayyuka, ciki kuwa har da kwangilolin naira bilyar 25 da ya bayar ba bisa ka’ida ba, da kuma yi masa yankan-baya.

Wannan wasika ce wasu su ka fallasa ta a ranar Talatar da ta gabata, inda su ka nuna Baru ya bayar da kwangiloli ba tare da tuntubar hukumar gudanarwar NNPC ko ogan sa Kachikwu ba. Wani abin lura a nan, Kachikwu shi ne kuma shugaban Mambobin Hukumar NNPC din.

Ranar Litinin da ta gabata, sai shi kuma Baru ya maida wa Kachikwu zafafan kalamai, inda ya bayyana cewa ai babu wata dokar da ta ce idan zai bayar da kwangiloli wai sai ya yi shawara ko ya nemi iznin Kachikwu.

Bayan nan kuma, Baru ya ce bai bayar da dukkan kwangilolin da Kachikwu ya rubuta wa Buhari cewa wai ya bayar ba. Ya kuma musanta cewa wai akwai harkalla da cuwa-cuwa a warin bayar da kwangilolin.

KUSKUREN SHUGABA BUHARI:

Rikici tsakanin Kachikwu da Baru ya faro ne tun a cikin watan Yuli, 2016, lokacin da Buhari ya cire Kachikwu daga shugabancin NNPC, ya maye gurbin sa da Baru.

Cikin Nuwamba, 2015, Buhari ya nada Kachikwu mukamin Karamin Ministan fan fetur. A lokacin ya rike mukamin shugaban NNPC da kuma Karamin Ministan Man fetur,m kafin a bai wa Baru NNPC.

To lokacin da Buhari ya nada Baru shubabancin NNPC, sai kuma ya wakilta Kachikwu a matsayin shugaban hukumar kula da NNPC.

ABIN DA DOKA TA CE

Doka ta ce hukumar gudanarwar NNPC ta na da alhakin duba ayyukan NNPC.

Doka ta nuna tilas ne Ministan Man Fetur ya kasance shi ne shugaban hukumar gudanarwar NNPC. Buhari ne Ministan Mai, sannan kuma doka ta ce ya na da damar ya nada wa wani iko na NNPC har ma shugabancin hukumar gudanarwar NNPC din. Wato kamar yadda ya yi wa Kachikwu.

Amma kuma dokar ta sake bai wa Buhari damar ya zama shugaban hukumar gudanarwar NNPC, yayin da mukamin wanda ya bai wa wannan iko kula masa da al’amurran NNPC ya na nan daram.

“Gudanar da ayyukan NNPC ya ta’allaka ne ga abin da sashen dokar NNPC na biyu ya nuna, wato cewa hakan ya rataya ne a wuyan hukumar daraktocin kamfanin, wadda shugaba ne zai kasance jagora.

“Shugaban Hukumar Daraktocin zai kasance Minista ne a cikin gwamnati.”

A takaice dai, doka ta kara nuna cewa kai ko da Ministan Man Fetur, Shugaba Buhari ya wakilta ko damka ikon sa na shugaban hukumar darktocin NNPC ga wani can daban, wato Ibe Kachikwu, zai iya ci gaba da zama shugaban hukumar daraktocin.

YADDA BUHARI KE MU’AMALA DA BARU, BA TARE DA SANIN KACHIKWU BA

Wannan ke musabbabin kwatagwangwama tsakanin Kachikwu da Baru Idan mai karatu ya yi nazarin bayanan Kachikwu da kuma martanin da Baru ya mayar masa, kamar kuma yadda PREMIUM TIMES ta samu cikakken bayanai, akwai hujjoji da ke nuna cewa Buhari na mu’amala kai-tsaye da Maikanti Baru, ba tare da sanin Ibe Kachikwu ba, wanda shi ne ya nada wakilin sa kuma ya ba shi ikon shugabantar al’amurran Baru.

Wannan batu kuwa Baru da kan sa ya tabbatar da haka, a cikin bayanin da ya yi jiya Litinin, inda ya ce shi ya na karbar umarni da amincewa ne daga Babban Ministan Man Fetur, kuma Shugaban Kasa, Buhari.

Cikin wasikar da Kachikwu ya aika wa Buhari a watan Agusta, ya ce lokacin da Buhari ke zaman hutun jiyya a Landan, tsakanin watan Mayu da Agusta, Baru ya yi ta kokarin ganin ya samu amincewar aiwatar da wasu ayyuka daga Mataimakin Shugaban Kasa, kuma Mukaddashin Shugaban Kasa a lokaci, Yemi Osinbajo – domin ya gudanar da wasu canje-canje masu yawan gaske a NNPC.

LAIFIN SHUGABA BUHARI

Shi kuwa Osinbajo ya umarci Baru da ya koma wajen Ibe Kachukwu domin ya ba shi iznin yin canje-canjen.

Maikanti Baru bai sake komawa ta kan Kachikwu ba, kuma bai aiwatar da canje-canjen ba, har sai bayan dawowar Buhari ranar 19 Ga Agusta, inda shi Baru ya bayyana canje-canjen sa a ranar 29 Ga Agusta.

Dalili kenan Kachikwu ya rubuta wa Shugaba Bauhari wasika, washegari a ranar 30 Ga Agusta, saboda Baru ya je ya bugi gaba ya gudanar da canje-canjen, wadanda shi kuma Kachikwu bai ma san an yi ba, sai dai a jarida ya gani.

A takaice dai Osinbajo a matsayin sa na lauya, ya san cewa kafin Baru ya gudanar da canje-canje a NNPC, tilas sai ya tuntubi hukumar daraktocin kamfanin, kamar yadda doka ta tanadar, amma shi kuwa Buhari bai yi wannan tsinkayen ba.
Ita ma jaridar Daily Trust ta ranar Lahadi da ta gabata, a shafin ra’ayin jaridar ta nuna cewa Shugaba Buhari ne ya haddasa wannan mummunan rikicin tsakanin Ibe Kachikwu da Maikanti Baru.

“Tambaya a nan wacce tilas a amsa ta, shin Shugaban Kasa ne ya amince Baru ya yi canje-canje kuma ya bayar da kwangiloli ba tare da mambobin hukumar daraktocin NNPC sun sani ko sun gani kamar yadda doka ta tanadar ba? Kuma su wa ne su ka yaudari Buhari har ya yi wannan kasassaba?”

“Buhari ne fa da kan sa ya kafa wannan mambobin hukumar daraktocin, don haka babu wani dalilin da zai sa ya aiwatar da wani abu tsakanin sa da Baru ta bayan fage, ba tare da sani ko sanar da mambobin ba.”

“Mun yi amanna cewa wannan gaba da kullatar juna sakamakon kauce wa bin tsarin dokoki da ta faru tsakanin Kachikwu da Baru, ta ruru ne sanadiyyar dawurwurar matsalar iya shuagabanci da gwamnatin Buhari ta nuna a cikin wadannan shekaru biyu da suka gabata.” Haka ra’ayin jaridar ya nuna.

Idan masu karatu ba su manta ba, irin haka ta faru tsakanin Ministan Shari’a Abubakar Malami da Shugaban EFCC, Ibrahim Magu, da kuma tsakanin Ministan Lafiaya Adebowale da dakataccen shugaban hukumar NHIS, Yusuf.

Dalilin irin wannan dawurwura ce lauya Femi Falana su ka bukaci Buhari da ya gaggauta sauka daga mukamin Babban Ministan Man Fetur

Share.

game da Author