Bukatu 6 da Kungiyar Musulmai ‘MURIC’ ke so gwamnati ta yi wa musulman Najeriya

0

Kungiyar kare hakkin musulmai a Najeriya ‘MURIC’ karkashin shugabancin Ishaq Akintola ta yi kira ga gwamnati da ta amince da wadansu sharudda da take ganin zai warware wasu dama da aka hana musulman kasar nan more su.

Akintola ya ce a irin mulki na demokradiyya da muke yi a kasar nan babu bai kamata ce har yanzu musulmai ba sa more ma wasu ababe da addininsu ya shirya musu a kasarnan.

Ya ce tarihi ya nuna cewa zuwan turawa Najeriya a karni na 19 ne farkon fara tauyewa musulmai wasu abubuwa da suke morewa na addini wanda turawan suka zo suka samu suna yi amma suka fifita shirin kiristanci akan su.

MURIC sun nemi gwamnati da ta amince da wadannan bukatu nasu guda 6.

1. Kira ga gwamnati ta mai da ranar Juma’a ranar hutu kamar yadda adinin kirista ke more ranar lahadi saboda musulmai su sami walwala wajen yin Ibadarsu.

2. Gwamnati ta mai da ranar 1 ga watan Muharram hutu a kasar nan.

3. Ya kamata gwamnati ta amince da shaidar takardan auren musulmai kamar yadda ta amince da na adinin kirista da shaidar kotu.

4. Ya kamata gwamanti ta gyara rigunan makaranta yara, soja, ‘yan sanda da sauran su yadda matan musulmai zasu iya fita kamar yadda addininsu ya shar’anta.

5. A daina hana mata daukan hoto na fasfo da hijabi ko kuma tilasta wa limami kwance rawaninsa ko kuma sai ya aske gemunsa domin hakan ya karya dokar addinin musulunci.

6. A kafa kotun shari’a a yankin kudu maso yammacin kasar nan saboda musulmai mazauna yankin.

Share.

game da Author