Cutar ‘Monkey Pox’ ta yadu zuwa jihohi 7 na kasar nan

0

Shugaban hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa Chikwe Ihekweazu ya ce akalla mutane 31 ne suka kamu da cutar ‘Monkey Pox’ daga jihohi 7 na kasar nan.

A lissafe jihohin sun hada da Bayelsa, Rivers, Ekiti, Akwa Ibom, Lagos, Ogun da Cross River.

Ihekweazu ya ce mai yiwuwa ne ba kowanen su bane ke dauke da wannan cuta na ‘Monkey Pox’ sai dai an ajiye su ne zuwa a kammala bincike.

Cutar ‘Monkey Pox’ ya yadu zuwa jihohi 7.inda bayan nan za mu san irin matakin da za mu dauka.”

” Duk da hakan babu wanda ya mutu cikin wadanda ke dauke da cutar sannan wasu cikinsu sun fara samun sauki daga cutar saboda samun kula a asibitocin da suke kwance.”

Daga karshe Ihekweazu ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankalinsu su kuma hanzarta kai duk wanda suke ganin ya kamu da cutar zuwa asibiti mafi kusa da su sannan kuma su guji shan magani batare da izinin wani ma’aikacin kiwon lafiya ba.

Share.

game da Author