Ibrahim da iyayen sa da sauran kannen sa, sun dade su na zaune a kauyen Kwarakwara da ke yankin Mambilla, cikin jihar Taraba. Shi da sauran mazauna yankin sun sha fama da rikice-rikicen kabilanci da na addini.
Nasir Ayitogo na PREMIUM TIMES ya yi tattaki zuwa yankin Mamabila domin ganawa da mazauna yankin da dauko wannan rahoto na musamman.
Sau da dama an sha kafsawa tsakanin kabilun cikin yankin Mambilla da kuma Fulani makiyaya da kan kai wa juna harin da kan haddasa kira da lalata dukiyoyi.
To su dai iyalan su Ibrahim ba su taba afkawa cikin irin wannan rikici ba.
Ma’ana bai taba shafar su ba, har sai ranar wata Asabar da dare, ranar 17 Ga Yuni, 2017, daren da wasu mutane dauke da adduna su ka kewaye garin Kwarakwara da ke cikin Karamar Hukumar Sardauna, su ka rika sara, suka da kisan jama’a.
Ibrahim mai shekaru 18 da haihuwa, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ya na kallo yayin da ya boye a kan wata bishiyar goro, aka yi wa mahaifin sa, mahaifiyar sa, kishiyar mahaifiyar sa da kuma kannen sa shida mata yankan rago.
“Wannan ce rana mafi muni a rayuwa ta.”
Haka Ibrahim ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Wannan mummunan kashe-kashe ya shafi kauyuka har 13 da su ka hada da:
Kwarakwara, Mayo Ndaga, Nguroje, Dorofi, Tamya, Hainare, Bang Three Corner, Chabbal Peluwaje, Labbare da Teb.
Akwai kuma irin su Mayo Dule da Tanviya. Shaidu da dama sun tabbatar wa Premium Times cewa akasarin wadanda aka kashe din duk Fulani ne.
Su dai ‘yan sanda sun ce mutane bakwai kawai aka kashe, to amma kuma Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah, ta ce ‘yan sanda makaryata ne. Miyetti Allah ta ce an kashe Bafulatani sun kai 351, ciki har da wasu iyalan Nguroje su 11.
Kungiyar ta kuma hakkake cewa wasu mutanen har 381, sun bace, wasu kuma babu labarin su. Ba a tabbatar da mutuwa ko kashe su aka yi. Ta kuma ce an hallaka shanu 20,000, wasu daga cikin wannan adadin, wasu da dama kuma sace su aka yi.
Har ila yau, Miyetti Allah ta ce an kona gidaje da bukkokin Fulani sama da 400.
Ita dai gwamnatin jihar Taraba ta ce yawan wadanda aka kashe ba su kai yadda ake yayatawa ba.
Wata ruwaya ta ce rikicin ya barke ne sakamakon ramuwar-gayyar wani hari da Fulanin da ke makwabtaka da wani yanki na Mambilla su ka kai. Ruwayar ta ci gaba da cewa an yi ta watsa labarin harin kwana da kwanaki, ta yadda zaman dardar ya tunzura kabilun yankin su ka dauki fansa kan Fulani.
Sai dai kuma wasu mazaunan yankin sun bayyana cewa abin da ya ruruta rikicin shi ne jami’an tsaro su ka kama wasu matasa na garin Nguroje, su ka zarge su da tayar da fitina da kuma cewa mambobi ne su na wata kungiyar matasa masu kashe-kashe da ke yankin na Mambilla.
Kan wannan kamu ne sai Mista Yeb ya jagoranci wasu matasan Mambilla zuwa Nguroje domin su tayar da boren rashin yardar su da kama matasan, su na masu cewa wai Fulani ne su ka sa aka kama matasan na Mambilla.
PREMIUM TIMES ta kira Mista Yeb domin ya kare kan sa daga zargin da aka yi masa, amma bai dauka ba. A lokacin an rigaya an dakatar da shi daga aiki, kuma lokacin da PREMIUM TIMES ta je Gembu domin ganawa da shi, wayoyin sa duk a rufe su ke.
Shi kuwa wani shugaban matasa a yankin mai suna Umar Abdulmumin, cewa ya yi sai da aka shafe kwanaki hudu ana karkashe su, ba a tsawatar ba. Kuma jami’an karamar hukuma da na jihohi ba wanda ya yi magana. Ba a daina kashe-kashen ba har sai da gwamnatin tarayya ta aika da sojoji da ‘yan sandan kwantar da tarzoma a yankin.
“Ban taba ganin mummunan kashe-kashe irin wannan ba.”
Wannan shi ne kalamin da kwamandan riko na runduna ta 3 ta Sojojin Nijeriya da ke Jos, Benjamin Ahanotu ya bayyana yayin da ya ziyarci yankin Mambilla.
“Kai ko Boko Haram ai ba su yanka mata da kananan yara. Amma a Mambilla an yanka kananan yara da mata masu ciki.”
Haka Birgediya Janar Ahanotu ya bayyana.
Amma shi kuma ya dora laifin a kan masu rike da sarautun gargajiya na yankin Mambilla da shugabannin yankuna saboda sakacin su na kasa hana rincabewar rikicin.
“Ta yaya ma za a ce ana rikici a kofar gidan basarake, ana yanka mutane ya na kallo amma ba zai iya tsawatarwa ba?”
“A matsayin su na shugabannin al’umma, ba su tsawatar an daina ba, ba su garzaya da wadanda su ka ji ciwo zuwa asibiti ba, ta yadda wadanda aka ji wa raunukan su ka gwamnmace su tsallaka kasar Kamaru ana yi musu magani.” Inji kwamandan sojojin.
Ya dora laifin kan ‘yan siyasa
An sha samun rikice rikice a yankin Mambilla tundaga wajajen shekarun saba’o’I, wato 1970s. an yi rikici cikin 1979, 1980, 1982, 2001 da kuma 2002. Dukkan wadannan rikice-rikicen sun faru ne tsakanin kabilun yankin Mambilla da kuma Fulanin yankin.
Tun da ake wadannan rikice-rikicen babu wata gwamnati da ta taba hukunta wadanda aka kama da aikata kisan.
Dubban jama’a sun rasa muhalli a rikicin 2002, yayin da wadansu kuma suka tsallake zuwa kan iyaka, kusan nisan kilomita 100 a cikin Kamaru.
Mambilla dai can ne za a yi aikin samar da hasken lantarki har migawat 3,050, wanda zai ci kudi har dalar Amurka bilyan 5.9. dangane da wannan rikici, sai wasu ‘yan siyasa su ka shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kirkiro rikicin ne domin a kashe wa gwamnatin tarayya guiwa ta yadda ko dai a kawo wa aikin kafar-ungulu ko kuma a fasa gudanar da shi.
Wani dattijon Mambilla mai suna Emmauel Njiwa, ya shaida wa Nasir Ayito na PREMIUM TIMES cewa gaba daya rikicin magana ce kan mallakar gonaki kawai.
Njiwa ya ce Fulani Fulani sun saye mafi yawan gonaki, ta hanyar dama ko iznin yin kiwo da gwamnati ta ba su, domin gwamnati ta killace su don ta san yadda za ta rika karbar jangali a hannun su.”
Sai ya kara da cewa a kwana a tashi bayan shekaru da dama, sai aka sauya takardar iznin yin kiwon da aka ba su zuwa takardar shaidar mallakar gonaki.
Sai dai kuma da yawan jami’an gwamnati da ke yankin Mambilla ba su yarda su yi hira da PREMIUM TIMES ba.
Shi kan sa Kakakin Majalisar Jihar Taraba, Abel Diya, kin yin magana da Premium times yay i, a bisa dalilin cewa tunda an rigaya an kafa kwamitin bincike, to bas hi da hurumin yin magana.
Yan gudun hijira
Wannan kashe-kashe ya haifar da ‘yan gudun hijira har kimanin 12,431, wadanda aka killace a sansanoni har 12.
Sai dai kuma duk yawancin wadanda ke sansanin Nguroje duk sun fice daga sansanin sun nemi mafaka a gidajen ‘yan uwa da abokan arziki saboda tsananin sanyi. Shi ma Ibrhaim Nguroje kasa zaman sansanin yay i ya nemi mafaka a wani gida.
Sauran sansanonin sun hada da na Gembu, Mayo Ndaga, Dorofi, Hainare, Tamnya/Tuwa, Bang 3 corner, Labarre, Kan Iyaka, Njawai da Mbamnga/Tavia.
Gwamnatin Najeriya dai ta aika da tulin abinci ga ‘yan gudun hijira ta hannun Hukumar Agajin Gaggawa, NEMA. Yayin da gwamnatin jihar Taraba ta kafa kwamitin binciken musabbabin rikicin.