‘Yan bindiga sun kai hari gidan Ibrahim Comassie a Katsina

0

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan tsohon Sifeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Comassie a garin Katsina inda suka budewa masu gadin gidan wuta.

Dan sanda daya ya mutu nan take sannan wani daya ya na asibiti ana duba shi.

‘Yan bindigan dai sun zo gidan Comassie ne da wajen karfe 8 na dare akan babur.

Share.

game da Author