Zan ci gaba da kwaikwayon Buhari ko baya gwamnati – Obinna Simon ‘MC Tagwaye’

0

Shahararren mai barkwancin nan wanda aka fi sani da kwaikwayon Buhari mai suna Obinna Simon ya ce ko bayan Buhari ya sauka daga shugabanacin Najeriya zai ci gaba da kwaikwayonsa domin Buhari shugaba ne da aka san dashi a duniya.

MC Tagwaye kamar yadda ake kiransa ya ce ya dade yana kwaunar Buhari a rayuwarsa wanda dalilin haka ne ya sa ya koyi yadda yake magana kuma ya fara kwaikwayonsa.

Duk da cewa Simon Obinna dan asalin jihar Anambra ne, an haifesa ne a jihar Katsina.

Ya ce ya fara sha’awar kwaikwayon Buhari ne tun bayan hira da akayi da shi a gidan Jaridar Saharareporters. Daga nan ne fa ya yi sha’awar fara kwaikwayon da.

Share.

game da Author