Kamar yadda aka sani ne cewa cutar Sankarau cuta ce da ta ke kama mutane musamman yara kanana ‘yan kasa da shekara 5 a lokacin zafi wanda hakan yakan kai ga a rasa yaran idan har cutar ta kama su kuma ba’a kai su zuwa ga asibiti cikin gaggawa ba.
A tsakanin watan Nuwamba zuwa Afrilu mutane da dama sun rasa rayukansu a dalilin yaduwar cutar.
Sakamakon wata kiyasi da ma’aikatar kiwon lafiya ta yi a dan kwanakinnan ta fitar cewa cutar ta kama mutane masu yawa a jijohin Zamfara, Kano, Katsina, Sokoto, Kebbi, Niger, Nasarawa, Jigawa, Abuja, Gombe, Taraba da jihar Yobe.
Hukumar kiwon lafiya na majalisar dinkin duniya da kasar Britaniya sun samar da alluran rigakafi da magunguna domin taimakawa jihohin da suke fama da annubar a kasa Najeria.
Jihar Zamfara
Kwamishanan kiwon lafiya na jihar Zamfara Suleman Gummi yace ctar sankarau din yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 160 a jihar.
Ya kuma kara da cewa akall kananan hukumomi 14 suke fama da cutar zuwa yanzu a jihar.
Kungiyar likitocin kasa Najeriya NMA da kuma mutane jihar Zamfara sun koka da yadda gwamnati take nuna musu halin ko in kula wajen samar da rigakafin ga ‘Ya’yansu da mutane baki daya.
Bayan haka kuma shagunan sai da magunguna a jihar suna cin karaen sub a babbaka domin suna siyar da su yadda suka ga dama.
JIHAR SOKOTO
Rahotanni sun nuna cewa mutane 41 suka rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar sankarau a jihar
Kwamishanan kiwon lafiya na jihar Balarabe Kakale y ace mutane 600 a cikin kanana hukumomi 8 a jihar sun kamu da cutar saboda rashin karban alluran rigakafin cutar.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar ta yanke shawaran da ta fara yin alluran rigakafi wa mutane 700 a kyauta domin hana yaduwar cutar.
Ya ce alluran suna yi wa yara da manya ‘yan shekara 1 zuwa 30 a duk kanan hukumomin da ke jihar.
JIHAR KATSINA
Jihar Katsina ma ta sanar da barkewar cutar a wadansu kananan hukumomin jihar.
Gwamnatin jihar aika ma’aikatan kiwaon lafiya zuwa kauyuka da birane domin samar da Rigakafi ga mutane musamman wanda basu kamu da cutar ba tukuna.
Gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi hira da wata likitan yara Adefunke Babatola akan illar cutar Sankarau inda ta shawarci mutane musamman uwaye mata masu goyo da kanana yara da su kai ‘ya’yansu su asibiti domin yin alluran rigakafi.
Ta kuma fadi hanyoyin biyar da za abi domin kiyaye wa daga kamuwa da cutar Sankarau da suka hada da
1. Yin allurar rigakafi.
2. Tsaftace muhalli.
3. Rage cinkoso a wuri daya.
4. Abude tagogi domin samun isasshen iska a dakunan da ake zama.
5. A daina ganin cutar Sankarau a matsayin wani tsafi ne ko jifa.
Likitar ta ba bayanai akan alamomin da ke nuna cewa mutum ya kamu da cutar sankarau kamar haka
Alamomin su hada da:
1. Za ka ga yaro yana ta suma idan ya kamu da cutar.
2. Yawan kwanciya da gajiya
3. Yawan yin Amai
5. Curar na kawo zafin jiki wanda daga baya yakan iya zama Zazzabi.
6. Mutum zai dinga ganin jiri
7. Sankarewan wuya.
8. Rashin son ganin haske.