Dubban magoya bayan sanata Ali Ndume yan sun fito zanga-zanga domin nuna kin amincewarsu da dakatar da sanatan daga ayyukan majalisa har na tsawon watanni shida.
Masu zanga-zangan sun rufe hanyoyin zuwa majalisar inda hakan ya sa hanyar bata biyuwa.
Suna kira ne da neman a janye dakatarwar da majalisa ta yi wa Sanata Ndume.
Gwamnan jihar Barno Kashim Shettima ya ziyarci Saraki a makon da ya gabata domin neman Shugaban majalisar ya sake duba wannan hukunci da ta dauka a kan sanata Ndume.
Majalisar dattijai ta dakatar da sanata Ndume ne saboda shine ya nemi majalisar da ta binciki badakalar siyan motar da ake zargin shugaban majalisar Bukola Saraki da siya ba tare da takardu na ainihi ba da kuma zargin cewa wai sanata Dino Melaye bai gama karatun jami’a ba.
Kwamitin da ta binciki wannan korafi sannan ta mika sakamakon bincikenta a zauren majalisar ta kuma sanar wa majalisa cewa sanata Ndume ya yiwa majalisar karya.
Kwamitin ta ba da shawarar a dakatar da Ali Ndume na shekara daya, in da bayan haka majalisar ta amince da dakatar dashi na wata shida.