A yau Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da babban mai tsaron lafiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a kotu.
Mai tsaron Shehin malamin mai suna Haruna Abbas, an gurfanar da shi ne tare da Ibrahim Musa da Adam Suleiman a gaban mai shari’a Adeniyi Ademola na Babbar Kotun Tarayya, Abuja.
An gurfanar da su ne a bisa wasu tuhuma guda takwas da ake zargin su da laifin da ya danganci “mara wa ta’addanci baya tsakanin 2009 zuwa 2013, ta hanyar tura mutane zuwa kasar Iran domin su koyo dabaru na aikata ta’addanci.”
Haka aka gabatar a Kotun.
Wannan laifi dai an ce ya saba wa doka ta Sashe na 4, na dokar hana ta’addanci ta 2013.
Da aka fara sauraren karar, lauya mai gabatar da kara Chike Nnenna, ya shaida wa kotu cewa, an sake sabon-lalen wannan shari’a ne domin tuhumomin da ake musu tun daga 5 Ga Nuwamba, 2014 ne.
Nnenna ta roki kotu da ta amince da tuhumomin da ake wa wadanda ake zargin domin su fara kokarin kare kan su.
Yayin da aka karanto masu tuhumar da ake musu, dukkannin su dai sun musanta aikata laifukan.
A karshe mai gabatar da kara ya nemi a dauke Ibrahim Musa daga hannun jami’an SSS a ci gaba da tsare shi a kurkuku.