Rundunar Sojin Najeriya ta saki mutane 593 bayan ta tabbatar da cewa basu da wata alaka da kungiyar Boko Haram.
Shugaban ‘Operation Lafiya’Lucky Irabo ne ya danka mutanen ga gwamnatin jihar Barno a wata taro domin hakan da aka yi a Maiduguri ranar Litini.
Shugaban ‘Operation Lafiya’ wanda Abdulrahman Kuluya ya wakilta yace sun yi hakan ne bisa ga umurni da shugaban sojin Najeriya Tukur Buratai ya bada.
Ya kuma ce sun saki mutanen bayan bangaren bincike na Sojin wanda ake kira da ‘Joint Investigative Team’ ta kamala binciken ta akan mutanen.
Irabo yace sun danka mutanen ga gwamnatin jihar Borno domin samun kula da za su bukata kafin su koma garuruwansu.
Bayan haka shugaban jin dadin mutane na jihar Borno Ladi Musa ta yi marhaban da wannan kokari na sojin Najeriya din.
Ta fadi hakan ne yayin da take karban mutanen a asibitin Bulumkutu Rehabilitation Center inda ta tabbatar wa sojojin cewa gwamnatin jihar Borno ta ware wuri na musamman domin kula da mutanen.