Tsohon dan takaran shugaban kasa a jam’iyyar NRC Bashir Tofa ya ki baiyana a Kotun shari’a da ke jihar Kano kan bashin da ake binsa na dala $200,000.
Tsohon ministan Karafa Bashir Dalhatu ne ya maka Bashir Tofa a kotu ya na neman kotu ta kwato masa bashin $200,000 da ya ba tsohon dan takaran shugaban kasa Bashir Tofa.
Bashir Dalhatu yace Bashir Tofa yayi alkawarin biyan sa kudin da ya bashi bashi a lokacin da yake kasar waje.
Alkalin Kotun ya da ga sauraren karan zuwa 10 ga watan gobe.
Bashir Tofa yace ya dauka wannan kudi kyauta ce Bashir Dalhatu ya bashi ba aro ba. Amma Bashir Dalhatu yace tun bayan sanar dashi cewa kudin ba aro ya bashi ba ya ki yin komai akai domin mai da masa da kudin sa.
Bashir Tofa ya bukaci ya biya kudin da nairan Najeriya amma Dalhatu bai amince da hakan ba.
Yanzu dai Bashir Tofa ya daukaka kara zuwa wata kotun ya na kalubalantar cewa kotun Shari’a bata da hurumin sauraren irin wannan kara.