Tonon Silili: EFCC ta kama naira miliyan 250 a kasuwan ‘yan canji

0

Hukumar EFCC ta kama wasu mutane biyu da makudan kudi a kasuwar canjin kudade da ke Balogun jihar Legas.

EFCC ta ce ta sami nasaran cafke mutanen ne bayan sun sami bayanai akan kokarin yin hakan da ga bakin wani da ya tona musu asiri.

Hukumar ta ce tsabar kudin da suka kama ya kai naira miliyan 250 kuma duk an canza su  zuwa kudin Euro da fan din kasar Britaniya.

Hukumar ta kara da cewa ta sami nasaran kama  mutane 2 da sukayi dakon kudin.

‘Yan canjin da EFCC ta tuhuma sun ce su ma wani maigidansu ne ya ce su karbi wadannan kudade domin samar da canjin su.

 

Share.

game da Author