‘Yan bindiga sun kashe mutum 9 daga cikin mutum 50 din da suka yi garkuwa da su daga kasuwar Madaka dake karamar hukumar Rafi a jihar Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa cewa maharan sun kashe wadannan mutane baya ga mutum 22 din da suka kashe a ranar da suka yi awon gaba da mutum 50 daga kauyen.
Idan ba a manta ba maharan sun yi garkuwa da mutum 50 inda da dama daga cikinsu mata ne daga kasuwar Madaka ranar Alhamis din makon jiya sannan sun kashe mutum 9 daga cikin su yayin da suke hanyar kai su maboyar su a dajin Allawa.
Hakimin Madaka Idaho Bawale-Madaka ya ce maharan sun kashe mutum bakwai a kauyen Kukoki dake karamar hukumar Shiroro sannan suka kashe wasu mutane biyu yayin da suke hanyar tafiya inda za su a jiye su.
Madaka ya ce zuwa yanzu sun yi jana’izan mutum sama da 30 da maharan suka kashe sannan har yanzu ba su kira sun bukaci kudin fansa ba.
Ya ce a cikin ‘yan kwanakin nan ya yi kokarin bin sawun maharan domin ceto mutanen dake hannun su amma abin bai yiwu ba.
Sarkin Kagara Ahmed Attahiru-Gunna da dan majalisar wakilai na kasa dake wakiltar Rafi/Shiroro/Munya Ismaila Modibbo sun ziyarci mutanen da suka ji rauni a dalilin harin dake kwance a asibiti tare da basu tallafi.
Discussion about this post