Rundunar sojin Najeriya ta ce ‘yan bindigar da suka kashe sojoji a jihar Delta sun kuma yi awon gaba da makaman su bayan sun kashe
Babban kwamandan runduna ta 6 ta sojojin Najeriya, Jamal Abdussalam, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin kasar, Laftanar Kanar Jonah Danjuma, ya bayyana.
Da yake magana a lokacin da Manajan Daraktan Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC), Samuel Ogbuku, ya kai masa ziyarar ta’aziyya a hedikwatar sashin da ke Barikin Fatakwal a ranar Alhamis, Manjo Janar Abdussalam, ya ce sojojin za su cigaba da farautar waɗanda suka aikata wannan mummunar aiki a wannan yanke har sai sun kamo su sun kuma kwato makaman da suka yi arce da su, su kuma an hukunta su.
Ya ce babban hafsan sojin kasa, Taoreed Lagbaja ne ya bayar da wannan umarni ga sojojin da ke aikin a wannan tsibiri.
Shugaban sojojin ya ci gaba da cewa sojojin za su ci gaba da kasancewa a cikin wannan ruwa har sai an kama waɗannan mutane da kuma kwato makaman da suma arce da.
A ƙarshe ya yi kira ga mutane da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri ta yadda za a kamo waɗannan ƴan bindiga sannan a kwato makaman da suka arce da su aka kuma hukunta su.
Discussion about this post