Tsohon Antoni Janar na Tarayya, kuma tsohon Ministan Shari’a, Micheal Aondoakaa, ya shaida wa kotu a ranar Alhamis cewa tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya yi ƙoƙarin ganin an sasanta tuhumar da ake wa tsohon Gwamnan Adamawa, Murtala Nyako, saboda yawan shekarun da ya ke da su.
Nyako wanda a yanzu ya ke shekaru 81, shi ne gwamnan jihar Adamawa, daga 2011 zuwa 2025.
Bayan an sake gabatar da Nyako a kotu, Aondoakaar, wanda shi tsohon jagoran lauyoyin da ke kare Nyako, ya shaida wa Mai Shari’a cewa akwai lokacin da Buhari ya umarci tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami cewa ya zauna da EFCC, domin a soke tare da janye tuhume-tuhumen da ake wa Nyako a kotu.
“To amma sai siyasa ta shiga cikin lamarin, a lokacin da ake tattanawar, saboda shi Malami a lokacin ya na son zama gwamnan Kebbi,” inji Aoandoakaar.
Wannan bayani da ya fito daga bakin sa, ya fito ne bayan da lauya mai gabatar da ƙara, Oluwaleke Atolagbe, ya shaida wa kotu cewa akwai ƙoƙarin da Nyako suka yi domin sasantawa a wajen kotu tare da gwamnatin tarayya.
Sai dai kuma nan da nan sai Aoandoakaa ya fayyace yadda batun ya ke, cewa batun “plea bargain” ɗin da Atolagbe ya ce an so a yi wajen kotu, bai faɗi maganar daidai ba. Domin hakan ya na nuna kamar Nyako ya amince da ya yi laifi kenan.
“Ina so na fayyace wa kotu yadda lamarin ya kasance a baya. Batun ba na sasantawa wajen kotu ba ne. Magana ce aka yi ta a sasanta. Amma sai Malami a lokacin bai samu ya yi hakan ba a matsayin sa na Antoni Janar, saboda a lokacin lokacin hankalin sa na kan siyasa. Ya so zama gwamnan jihar Kebbi,” inji Aoandoakaa.
Bayan da Nyako wanda ake tuhuma ya bayyana wa kotu cewa bai aikata laifin da ake tuhumar sa da aikatawa ba, sai Mai Shari’a bada belin su bisa sharuɗɗan belin baya.
Mai gabatar da ƙara bai nuna tirjiyar rashin yarda da bada belin na su ba.
Daga nan aka ɗage shari’ar zuwa 10 ga Mayu, 2024, domin yanke hukunci.
‘An Nemi Kashe Ni’ – Nyako:
Lokacin da ake karanto wa su Nyako tuhume-tuhume 37 da ake masu, sai ya yi farat daga inda ya ke tsaye, ya ce an nemi kashe shi, sau huɗu ana kai masa farmaki ba a yi nasara ba.
Ya yi wannan zargin ba tare da bayyana sunayen mutanen da ya ce ke shirya tuggun kashe shi ɗin ba.
Ya ce saboda abokan gabar sa sun kasa yin nasara a kan sa, sai suka rugungunto zuwa kotu, ɗauke da canje-canjen tuggu da kutunguila.
“Ban san komai a kan dukkan waɗannan canje-canjen da ake yi min ba.” Haka ya faɗa cikin fushi, kuma da ƙarfin murya.
“Ka na so ka tura ni kurkuku na mutu a can?” Haka ya shaida wa Rajistara na kotu, lokacin da ake karanto masa caje-cajen da ake yi masa.
Har sai da ta kai ɗan sa, tsohon sanàta, Abdul’aziz Nyako tausasa shi da ba shi haƙuri, sannan ya huce.
Discussion about this post