Mai magana da yawun tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Ruafai, Muyiwa Adekeye ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufai ya ziyarci ofishin SDP ne ba wai don wata tafiya ta siyasa ba.
Adekeye ya ce El-Rufai ya ziyarci shugaban jam’iyyar Shehu Gadam a ofishin jam’iyyar wanda abokin sa amma ba wata siyasa ba.
” Gabam ya kai ziyara gidan El-Rufai, shine shima ya kawo masa irin wannan ziya a ofis.
” Gabam da Nuhu Ribadu, sun ziyarci El-Rufai a gida sun yi buɗe baki tare, me yasa ba a ce Gabam ya ziyarci El-Rufai don ya koma APC bane tunda El-Rufai ɗan APC ne.
Ya hori mutane su yi watsi da raɗeraɗin wai ziyarar siyasa ce.
Discussion about this post