A wani ra’ayi da PREMIUM TIMES ta buga mai ɗauke da alhini da takaicin mummunan kisan dabbancin da tsagerun Delta suka yi wa sojojin Najeriya 17, jaridar ta ce babban aikin da ke hannun jami’an tsaron Najeriya, shi ne a tabbatar da an kamo waɗanda suka yi wannan mummunan kisa, kuma a hukunta su.
Cikin bayanin da jaridar ta buga, ta bayyana cewa daga cikin sojojin 17 da aka kashe, an guntile kawunan 14, sannan aka farke cikin su aka cire zuciyar kowanen su. Kuma aka cire wa kowane azzakarin sa.
A cikin ra’ayin jaridar mai taken Munin Kisan Gillar Da Tsagerun Delta Suka Yi Wa Sojojin Najeriya, akwai kaɗan daga bayanan jaridar kamar haka:
“Babban adalcin da za a yi wa sojojin Najeriya da tsagerun Delta suka kashe, shi ne ko ta halin ƙaƙa a tabbatar da kamo makasan, kuma a hukunta su. Ta haka ne za a iya kawo ƙarshen irin wannan mummunan kisan dabbancin da aka yi wa jami’an tsaron da ke sadaukar da rayuwar su wajen kare rayuka da lafiyar ‘yan Najeriya.
“Ɓoyayyun hujjoji sai ƙara bayyana suke yi, dangane da mummunar ranar da matsalar tsaro ta ƙazamce ƙasar nan, yayin da aka yi wa sojojin Najeriya su 17 mummunan kisan gilla, a hannun tsagerun ƙauyen Okuama cikin Jihar Delta, a ranar 14 Ga Maris.
“Ba mummunan kisa kaɗai aka yi wa sojojin ba, bayan an kashe su, an guntule kawunan 14 daga cikin su. Kuma aka farka cikin su, aka fizgo zuciyar kowanen su. Ba a nan wannan dabbanci ya tsaya ba. Sun kuma bi gawarwakin sojojin ɗaya bayan ɗaya sun guntule al’aurar su. Ƙololuwar kisan dabbanci kenan.
“Yayin da wannan bala’i ya zo daidai lokacin da masu garkuwa da kuma Boko Haram ke ƙara maƙasura, inda aka sace sama da mutum 500 na ɗalibai da masu gudun hijira a Kaduna da Barno, hakan na nuni da irin jan aikin da ke gaban manyan jami’an tsaron ƙasar nan.
“Amma kuma babban darasin da kowa zai ɗauka a wannan mummunan yanayi, shi ne, ba wanda zai iya bugun ƙirji ya ce shi dai wannan bala’i ba zai iya ritsawa da shi ba.”
Discussion about this post